BusinessLife Style
Trending

AIKI SAI MASU KAYAN AIKI, DOGARO DA KAI SAI HORARRU

AIKI SAI MASU KAYAN AIKI, DOGARO DA KAI SAI HORARRU !!

Ina matasan ENGAUSA, da kungiyoyi, da iyaye masu daukar nauyin matasa, dake yawan yin korafin shan wahalar samo ingantattun kayan aikin (wato Toolbox ) da suka dace su sayo, domin aiwatar da abin da aka koya a ENGAUSA HUB, kafin ilim ya rozaye ?

ENGAUSA ta yi binciken kwakwaf domin cika wannan buri nasu, har ta samar da TOOLBOX mai dauke da kusan dukkan abin da ENGAUSASHSHEN dalubin ke bukata wajen kafa na’urorin ELECTRICAL/ELECTRONICS, kamar su CCTV, SOLAR, ELECTRIC WIRING/FENCING, SATELLITE TV, har ma da gyaran circuit boards.

Abin sha’awar a wannan TOOLBOX shine, ta tattaro kusan dukkan matsakaitan kayan aikin site din ELECTRICAL ELECTRONICS, a takaice, kuma cikin karamar akwati mai saukin dauka. Ta hado da Guduma, Filaya kala biyu, Ranchi domin maye gurbin sifanoni masu yawa, Stripper domin feke cable, Digital Multimeter, Wuka tare da rezozin ta domin canjawa idan ta duskure. Hatta Soldering Iron da Socker da dalma na aikin electronic circuits, ba’a bar su a baya ba. Ga Allen Keys da Digital Tester, da Salatif, kunshe cikin wannan akwati mai kyawun gani da kwarjini, domin karfafa gwiwar kwastomomi.

Kuma duka a kan farashin naira dubu talatin ( N35,000). Amma daga kawo su daga Lagos, har sun kusan karewa. Wanda ha hanzarto zai samu cikin wannan farashin, domin bamu da tabbas din samo su cikin sauki haka idan mun bukaci karin supply daga Lagos.

Akwai CLAMP METER mai AC/DC, wacce ita dabantake, domin masu aikin Solar da ELECTRIC WIRING za su bukace ta don inganta sabon aiki ko don gyara tsohon aiki. Saidai ita kadai, naira dubu arba’in da biyar ce ( N45,000).

Allah Ya sanya albarka cikin sana’oin ku. Allah albarkaci horon da ku ka samu har ku tsaya da kafafun ku, ku dauki wasu aiki.

hamzat abdulroqib

my name is Abdulroqib Hamzat I am a blogger and an online marketer. My blogs are mostly covering topics on Technology and tip about SEO, I am a graduate of Engausa global tech hub.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button